FA’IDA TA HUDU NA DARASIN AL-MILAL WAN NIHAL
HALASCIN TSINEWA YAZID DA KAFIRTA SHI A WAJEN WASU MALAMAN SUNNAH
ALLAMAH JALALUDDIN SUYUDI YA TSINE MA YAZID A TARIKHUL KHULAFAH DIN SHI
Bukhari da kan shi ya rawaito wannan riwayar kamar yanda Jalalud Din Suyudi ya rawaito yake fadi.Allamah Jalalud Dini Suyudi yana cewa “Bukhari ya fitar,haka Annasa’iy da Ibn Abiy Hatim a tafsirin shi kuma lafazin na Ibn Abi Hatim ne daba’an amma duka su ukun suka rawaito daga hanyoyi daban daban cewa Marwan yayi hukunci a Madina alhali yana Wali wato gomna a Hijaz.Sai ya tashi yana huduba yana cewa: “Hakika Allah ya ganin ma Sarkin musulmi Mu’awiya dan Abi Sufyan ra’ayi mai kyau dangane da danshi Yazid-kenan nada Yazid aikin wane ne?yana nufin Allah ne yace a nada Yazid,wa ya isa yayi inkari ko yayi mu’arada saboda yayi mafarki-In ya halifantan dashi,to hakika Abubakar da Umar sun halifantar.A wani lafazi daban SUNNATU ABI BAKAR WA UMAR kamar yanda muka gani a riwayar Hakim.Sai AbdurRahman dan Abibakar yace SUNNATU HAIQAR WA KAISAR wato sunnan Haiqar da Kaisar dai.Sai AbdurRahman ya cigaba da fadi cewa hakika wallahi Abubakar bai kalifantar da daya daga cikin ‘ya’yan shi ba,kuma bai sa mutane su zabe mutanen gidan shi ba.Kuma shi Mu’awiya da ya nada danshi Yazid ko ya zaba ma mutanen gidan shi ne saboda jin kai da tausayi da bin umurnin shi.Sai Marwan yace ma AbdurRahman dan Abubakar ashe ba kai ne wannan wanda kace wa iyayen ka tir da ku ba?
Sai AbdurRahman yace “ALASTA IBNAL LA’IN ALLAZIY LA’ANA ABAKA ALA LISANIN NABIY WA ALIH”wato ba kai ne dan la’anannen ba wanda Annabi(sawa) ya la’ani mahaifin ka?Sai A’ishah (r) tace Marwan yayi karya,ba akan shi wannan ayan ta sauka ba,WALA KIN NAZALAT FI FULAN WA FULAN –da man Bukhari ya saba bai fadin sunayen mutane saidai yace Fulan da fulan amma in ka je Fathul Bari zaka ga waye Fulan da Fulan di.
Sai A’ishah ta cigaba da cewa saidai Allah ya la’anci mahaifin Marwan alhali Marwan na cikin tsatson mahaifin shi.FA MARWAN BA’ADU MAN LA’ANAHULLAH wato saboda haka Marwan sashi ne na wanda Allah(t) ya tsinewa ma,kuma sashi ne na wanda Annabi ya la’anta”.
Irin wadannan riwayoyin suna da yawa kamar yanda ma’abucin Musdarak Alas Sahihain yake fadi-wato Hakim kenan-Yana cewa Allah Subhanahu wa Ta’ala yayi yawa da irin wadannan riwayoyin.Saboda haka ban da lokacin kawo gabaki daya amma akwai su a Al-Musdaraku Alas Sahihaini da Ila akhirihi da sauran su.
Yanzu zamu koma zuwa ga Tarikhul Kulafa na Allamah Jalulud Din Suyudi kamar yanda muka yi alkawari,sannan mu komo mu yi magana akan Mu’awiyah dan Yazid wato salihin dan Yazid wanda ya ki ya amshi kalifanshi kuma ya rasu bayan kwana arba’in ko wata biyu ko uku akan sabanin riwayoyi,daga lokacin da Yazid ya rasu.
Allamah Suyudi yana cewa:LA’ANALLAHU QATILAHU-wannan ba halatta bane yayi ne-Wato Allah Ya la’anci makashin shi (wato Husain(as))WABNA ZIYADIN MA’AHUM,ma’ana Allah kuma ya la’anci Ibni Ziyad tare da wanda ya kashe Husain,WA YAZIDA AIDAN,da Yazid kuma.Ya cigaba yana cewa:WA KANA QATLAHU BIL KARBALA-Ba ina so in karanta komai da komai bane.Sannan sai yace WA LAMMA QUTILAL HUSAIN wato a lokacin da aka kashe Husain(as)-duk wannan a cikin Tarikhul Khulafah ne na Allamah Suyudi ne za a same shi-sai duniya ta canja da aka kashe Husain (as)-wannan shine abin da Nasibiy ba zai karba,a rike wannan sosai Nasibiy ba zai amsa wannan ba akan cewa duniya ta yiwa Husain kuka.Shahid guda daya da nake so in kawo akan wannan kafin in cigaba shine cewa : “Sa’alam ya fitar a cikin Amalihi daga Ali Kayyad Alkandiy yace na zo Karbala sai na cewa wani mutum daga masu daraja daga cikin larabawa cewa bani labarin abin da na dinga jin labari kafin in zo nan akan cewa kuna jin kukan aljanu a ran da aka kashe Imam Husain,sai yace a nan garin dai ba zaka hadu da kowa ba face sai ya baka labarin ya ji ba wannan kukan aljanun ba a ran da aka kashe Imam Husain.Wannan kenan amma Nasibiy ba zai yarda da wannan ba,kuma bai cuci Husain (as) ba don Nasibiy bai karba ba.
Akwai wadanda sama da kasa suke ma kuka,Allah na cewa FAMA BAKAT ALAIHIMUS SAMA’U WAL ARDU WAMA KANU MUNZARIN wato saboda haka sama da kasa basu masu kuka ba kuma ba su kasance daga wadanda ake saurara mawa ba,kenan sama da kasa suna yiwa wasu kuka tunda wadannan mutanen Fir’auna din su sama da kasa basu masu kuka ba-Allah bai yin lagawu,ba zai ce ba a yi kuka ba in ba a yin kuka-ba zai yiwu ba in da ace sama da kasa basa yi wa wasu kuka sai Allah yace su wadannan sama da kasa ba suyi masu kuka ba.KAM TARAKU MIN JANNATIN WA UYUN,WA ZURU’IN WA MAKAMIN KARIM WA NA’AMATIN KANU FIHA FAKIHIN,KA ZALIKA WA AURASNAHA QAUMAN AKHARIN,FAMA BAKAT ALAIHIMUS SAMA’U WAL ARDU WAMA KANU MUNZARIN-wannan QAUMAN AKHARIN din na Suratul Dukhan Allah yayi mana bayanin su a Shu’ara yana cewa FA AKHRAJNAHUM MIN JANNATIN WA UYUN,WA KUNUZIN WA MAKAMIN KARIM,KAZALIKA WA AURASNAHA BANI ISRA’IL-QAUMAN AKHARUN din sune Banu Isra’il.Wa’yanda aka gadar wa bayan halakar da Fir’auna da mutanen shi.
Kenan sama da kasa basu yiwa Fir’auna da mutanen shi kuka ba,me yake nufi kenan ?akwai wadanda sama da kasa suke ma kuka.Haka ya faru akan Husain (as)lokacin da kashe shi sama tayi kuka,haka yana faruwa wato TAGAYYIRAT KAUNIYYA masu yawan gaske sun faru.
Sannan ya zo akan cewa (duk dai a cikin Tarkhul Khulafa na Allamah Suyudi)mai riwaya na cewa:Na kasance a inda Umar Ibn AbdulAziz sai wani mutum ya ambaci Yazid da cewa Amirul Mu’uminina Yazid yace,sai Umar dan AbdulAziz yace mashi Yazid kake ce ma Amirul Mu’uminin?sai ya bada umurni dangane da wannan mutumin aka yi mashi bulala ishirin (saboda yace ma Yazid Amirul Mu’uminina).
Allamah Suyudi ya cigaba da cewa:Yazid ya firgita mutanen madina.A shekara ta sittin da uku labari ya je ma Yazid cewa mutanen Madina sun fita akan shi(sun fita akan shi wato sun yi masa tawaye),sai ya aika masu da runduna.
….Mu hadu a Jalasa ta gaba domin cigaban bayanin Allamah Suyudi.288
2 Maris 2016 - 15:27
Lambar labari: 738477
NA SHAIKH HAMZAH MUHAMMAD LAWAL YUSUF SULAIMAN YA RUBUTA